Tsaro

Illela: An kama wani da ya halarci bikin ɗan uwan shi a matsayin mai taimakawa ƴan ta’adda

Idan dai masu karatu basu manta ba, jami’an tsaron haɗin a karkashin jagorancin rundunar yan Sandan Najeriya a karshen watan da ya wuce sun kai samame a lunguna da sakon na maboyar yan ta’adda a faɗin jihar Sokoto, cikin har da Garin Gudun-Gudun dake karamar hukumar Illela.

Wannan arrow ko kibiya da ku ka ga anyi acikin hoto na daya, hoton wannan yaron ne da ku ka gani a cikin hoto na biyu dake dama.

Atakaice dai wannan yana cikin mutum 37 da sashen Hausa na BBC suka bada rahoton cewa an kama yaran turji a jihar Sokoto, hoton na dauke shi a ranar 01/01/2021 a wata majalisar da yaron mai suna Munsur suke shan shayi.

Advertisement

Haka zalika, hoto na biyu Arewa Times Hausa ta same a shi a yau da rana bayan wani ya ci karo da shi a wata jarida wacce ba Arewa Times Hausa ba.

Yan uwa da abokan arziki sun yi kukan zuciya haka kuma sun zubar da kwalla da ganin wannan hoto.

Wannan bawan Allah Abokin wasu matasan karamar hukumar mulki ta Illela ne kuma sananne anan garin Illela.

Ba yada hannu da wannan ta’addanci kawai kadai kaddara ce ta hau kansa.

An bayyana cewa yaron ya je bikin wani dan gidan su ne a can Gudun-gudun, amma sai akayi dai-dai da wannan samamen na jami’an tsaro ya rutsa da shi.

Advertisement