Tsaro

Illela: Ƴan bindiga sun sace mutum 8, suka kashe 1 a agarin Ambarura

Yan bindiga sun sake kai hari a garin Ambarura dake cikin laramar hukumar Illela, jihar Sokoto.

Wasu rahotannin da muke cigaba da samu na nuna cewa wasu mahara bindiga waɗanda ake kyautata zaton cewa yan ta’adda Fulani ne masu garkuwa da mutane ne sun sake afkawa garin na Ambarura a daren jiya Assabar.

Wasu bayanai na cewa maharan sun afkawa garin ne da misalin karfe 2:0 zuwa 3:0 na dare.

Advertisement

Wata majiya mai tushe ta tabbatarwa Arewa Times Hausa cewa yan bindigar sunyi garkuwa da mutane akalla 8, kuma suka kashe mutum 1.

Idan dai ba’a manta ba, ko a kwanakin baya dai yan bindigar sun yi garkuwa da yan uwan ɗan majalisar dokokin jihar Sokoto Honourable Bello Isah, mai wakiltar karamar hukumar Illela, amma daga bisani yan bindigar sun sako su bayan an su biya miliyoyin Naira.

Advertisement