Labarai

Hukunta Isra’ila Ya Zama Dole Don Hana Ƙarin Rashin Zaman Lafiya – Iran

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Nasser Kanaani ya ce Tehran ba ta neman kara ruruta wutar rikici a yankin amma ta yi imanin “hukunta Isra’ila ya zama dole” don hana ci gaba da rashin zaman lafiya.

Sauran abubuwan da Kanaani ya ce:

Kisan da aka yi wa Isma’il Haniyeh a Tehran ya saba wa dokokin kasa da kasa.

Iran tana da hakkinta na kare tsaron kasa da kuma ikonta a kan filayen ta.

Tehran na da hakkin ladabtar da Isra’ila, da hana ta, da kuma dakatar da laifukan da take aikatawa.

Tun da farko wani rahoto daga kafar yada labaran Amurka Axios ya nakalto wasu majiyoyi uku da ba a bayyana sunayensu ba na cewa sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya shaidawa takwarorinsa na G7 a taron da suka gudanar cewa Iran da Hizbullah za su iya kai hari kan Isra’ila tun a yau.

G7 – wadanda suka hada da Kanada, Faransa, Jamus, Italiya, Japan da Birtaniya – sun fitar da wata sanarwa da ke nuna “damuwa mai zurfi game da karuwar tashin hankali a Gabas ta Tsakiya” tare da yin kira da a kame daga kowane abinda zai ta azzara yanayin da ake ciki.