Siyasa

Hukumar tsaro ta farin kaya ‘DSS’ ta gayyaci wasu na hannun damar Gunduje

Hukumar tsaro ta farin kaya ‘Department of State Security’ (DSS) ta gayyaci wasu manyan na hannun damar Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Dukkan bayanai da Arewa Times Hausa ta samu daga majiyoyi sun bayyana cewa mutanen sun kai kan su gaban DSS bayan amsa goron gayyatar hukumar bisa zargin su da hannu a cikin harkar dabar siyasa a jihar Kano.

Bugu da kari, Kwamishinan Kananan Hukumomi na jihar ta Kano, Mallam Murtala Sule Garo, shima ya tabbata da wannan labarin, inda yace yana cikin manyan jami’an gwamnatin jihar da suka mika kan su ga hukumar DSS kamar yadda hukumar ta bukaci su bayyana a gaban ta.

Advertisement

Daga manyan na hannun damar Ganduje da aka gayyata a DSS sun hada da Fa’izu Alfindiki, shugaban karamar hukumar Birnin Kano; Khalid Ishaq Diso, shugaban karamar hukumar Gwale; da Injiniya Bashir Kutama, shugaban karamar hukumar Gwarzo.

Haka zalika, Kwamishina Murtala Garo yace an gayyaci mutumin da ke muradin son jam’iyyar APC ta tsayar da shi a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar ta Kano a zaben 2023 mai zuwa, A.A Zaura; da shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa; da shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi, da kuma wani mai bai wa Ganduje shawara.

Rahotanni da dama sun bayyana cewa ana zargin wasu daga cikin mutanen da DSS ta gayyata da hannu a manyan-manyan hare-haren ƴa daba, lamuran da suka yi sanadin mutuwar wasu mutane a jihar.

Amma, kawo zuwa lokacin hada wannan rahoto, mun samu bayanai da ke nuna cewa an sallami mutane dukkan su.

Advertisement