Taskar LabaraiTsaro

Hukumar Sojojin Najeriya Ta Gargadi Sojoji Akan Kada Su Yiwa Gwamnatin Buhari Juyin Mulki

Hukumar rundunar sojojin Najeriya karkashin jagoranci Ibrahim Attahiru da kada sojoji su hambarar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sannan hukumar ta nesanta kanta da kiran da waau ke yi na sojoji su karbe ragamar mulkin Najeriya.

Hukumar sojin ta sake nanata cewa ba karamin laifi ne mutum yayi yunkurin kawar da gwamnatin farar hula, sannan ta kara da nanatawa da babbar muryar duk wanda aka samu yana hada kai da wasu mutane masu son ayi juyin mulki zai fuskanci hushin hukuma.

Rundunar sojojin ta kara jaddada goyon bayan ta gwamnatin Buhari a jiya Litinin.

Mai magana da yawun hukumar Brigadier General Onyema Nwachukwu, shine yayi wannan jawabin a babban birnin tarayya Abuja.

Nwachukwu yace sun lura da cewa akwai masu bada shawarar cewa gwamnati mai ci a juya ragamar ta zuwa ga hukamar soja domin yin wasu canje-canje a kasa.

Ya kara da cewa hukumar soja zata cigaba da kasancewa wacce bata shiga harkokin siyasa a koda yaushe.

Back to top button