Tsaro

Hukumar NDLEA ta kama jabun kuɗi dala miliyan $4.7 a Abuja

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a ranar Lahadi, ta ce jami’anta da sanyin safiyar Juma’a, 18 ga watan Fabrairu, 2022, sun kama wani kaya da aka aika daga Legas zuwa Abuja a unguwar Abaji da ke babban birnin tarayya Abuja.

Advertisement

Femi Babafemi, Darakta, Media & Advocacy, hedkwatar NDLEA, Abuja, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, yace jami’an sun dakile yunkurin wata kungiyar hadin guiwa na sace akalla Naira biliyan ₦2.7 na tattalin arzikin Najeriya ta hanyar tura kudaden jabu na Dala miliyan $4.7 cikin al’umma.

Hukumar ta ce yadda aka yi nasarar isar da kudaden na jabun dalar Amurka da suka kai dala $4, 760, 000.00, ya sa aka kama babban wanda ake zargi, Abdulmumini Maikasuwa mai shekaru 42 da haihuwa.

Advertisement

A cewar shi, kwace kuɗin ya biyo bayan bayanan sirri da rundunar babban birnin tarayya Abuja ta samu, inda aka yi karin bayani kan motsin kudaden da kuma motar da ta kai.

Shugaban Hukumar NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya bayar da umarnin a mika kudaden da kuma wanda ake zargin da ake tsare da su zuwa ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, domin ci gaba da bincike.

Advertisement