Hukumar Kwastam Zata Rabawa Yan Najeriya Kayan Abincin Da Ta Kwace
Dangane da halin kuncin da kasar nan ke ciki, hukumar kwastam ta Najeriya NCS, ta bayyana shirin raba kayan abincin da aka kwace ga ‘yan Najeriya.
Shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce za a raba kayan abincin ne bayan an ba su takardar shaidar za’a iya cin su.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Kwastam, Abdullahi Maiwada ya fitar a ranar Talata, Adeniyi ya jaddada aniyarsa na ciyar da shirin samar da abinci na shugaba Bola Tinubu gaba.
“Bugu da kari, domin rage wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta da kuma inganta hanyoyin samun kayan abinci masu mahimmanci, Hukumar Kwastam ta Najeriya za ta taimaka wajen rabar da kayan abincin da aka mallaka kai tsaye ga Gwamnatin Tarayya.
“Waɗannan abubuwa za a basu shaidar dacewa don amfani da su daga hukumomin da abin ya shafa, kuma za a bada su ga talakawan Najeriya a duk faɗin ƙasar ta hanyar rabon adalci a yankunan mu da muke ayyuka,” in ji shi.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana lokacin da shirin za a fara rabon kayayyakin ba.