Lafiya

Hukumar Kwastam ta kama buhunhunan naman jaki guda 1,390 a Kebbi

Hukumar hana fasa ƙwaurin kayayyaki ba bisa ka’ida ba a Najeriya ta kwastam ta sanar cewa jami’an sun samu nasarar kama buhunhunan naman jaki guda 1,390 a Jihar Kebbi da ke a Arewacin Najeriya.

Shugaban hukumar (Kwanturola) wanda ke kula da shiyyar Kebbi, Joseph Attah, ya sanar cewa darajar kuɗin naman na jaki da suka kama ta kai naira miliyan ₦42,000,0000,000.

“Ɗaya daga cikin mutanen da hukumar ta cafke da naman na jaki ya bayyana cewa sai da suka yanka jakuna kimanin guda 1,000 kafin su samu irin adadin wannan naman da hukumar kwastan ta cafke,” inji Attah.

Advertisement

Ya kuma cigaba da cewa safarar naman na dabbobin da aka bayyana a matsayin waɗanda ba na ci ba ya saɓawa sashen doka na 63 (b) na kundin dokar hukumar ta kwastan.

Advertisement