Siyasa
Hukumance: Tambuwal ya shiga takarar shugaban kasa a 2023

Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Tsohon kakakin majalisar wakilai zai tsaya a karkashin jam’iyyar PDP.
Tambuwal ya bayyana hakan ne da yammacin ranar Litinin bayan taron masu ruwa da tsaki a Sokoto.
Gwamnan ya yi alkawarin gyara matsalolin da Najeriya ke fuskanta yayin da ya yaba wa kansa kan shugabanci nagari ba tare da tuhumar cin hanci da rashawa ba.
Tambuwal ya rasa tikitin takarar shugaban kasa na PDP a 2019 a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.