Siyasa

Hukumance: Okorocha ya shiga sahun cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na 2023

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bi sahun masu neman kujerar mai lamba ɗaya a Najeriya inda ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Wannan sanarwar ta fito ne a ranar Laraba cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar.

Okorocha  ya kara bayyana cewa zai gudanar da taron manema labarai a ranar Litinin 31 ga watan Junairu, 2022, domin tattaunawa da yan Najeriya game da takarar sa.

Advertisement

Wasikar tace, “Kamar yadda kuka sani, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta bayyana jadawalin gudanar da babban zaben shekarar 2023, ciki har da na ofishin Shugaban Tarayyar Najeriya.

“Yayin da zabe ke kara kusantowa a kwanaki masu zuwa, ‘yan kasarmu sun damu da ingancin mutanen da za su tafiyar da al’amuran al’ummarmu, wadanda za su iya magance wasu manyan matsalolinsu da suka hada da;

“Dan Najeriya wanda baya nuna kabilanci wanda zai iya hada kan kasarmu.

“Shugaba mai tausayin zuciya, wanda zai kula da talakawan kasarmu.

“Shugaba mai hangen nesa wanda zai iya samar da arziki ga dimbin al’ummarmu, ta yadda zai magance matsalolin talauci, rashin tsaro da tawayar matasa.

“Sakamakon wannan damuwar ne nake son gudanar da taron manema labarai na duniya kan aniyata ta tsayawa takarar shugabancin kasarmu Najeriya, inji Okorocha.

“Saboda haka, ina so in nemi addu’ar ku kamar yadda na bayyana nufina.”

Advertisement