Tsaro

Hotunan sojan Najeriya da wani dan sanda ya kashe a Borno bayan yayi tatir da giya

Sojan mai suna Marigayi Donatus Vonkong, wanda mai tsaro ne ga Abubakar El-Kanemi, Shehun Borno, dake a fadar sarkin lokacin da dan sandan ya kashe shi. An ce dan sandan ya sha barasa ne a lokacin da yayi harbin da ya kashe Donatus.

A cewar rahotanni, dan sandan ya fara “mummunan hali” a kusa da fadar kuma marigayin wanda shine shugaban sashin tsaro a fadar yasa baki.

Vonkong dai an ce Shehu ne ya zabo shi a matsayin babban jami’in tsaro tun a shekarar 2012 lokacin da aka ce ya ceci sarkin daga wani dan kunar bakin wake.

Advertisement

El-Kanemi ya tsallake rijiya da baya bayan tashin bam din da ya tashi bayan sallar Juma’a a wani masallaci da ke kofar fadarsa. Kimanin mutane 10 ne suka mutu a fashewar.

Advertisement