Al'ummaTsaro

Hotunan Gwamna Matawalle Sanye da Uniform na Sojoji

Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara Dakta Bello Matawalle kenan a wadannan hotunan sa sanye da kakin sojoji a ziyarar da ya kai wa sojojin da suka samu raunuka a cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Gusau babban birnin kasar.

Idan dai za a iya tunawa, sojojin Najeriya sun yi musayar wuta da wasu ‘yan bindiga a wani kauye da ke karamar hukumar tsafe.

Harin na baya-bayan nan ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama da ba su ji ba ba su gani ba tare da jikkata wasu da dama.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Gwamna Matawalle ya tabbatar wa sojojin cewa zai samar da dukkanin magungunan da suka dace don warkar da sojojin da suka samu raunuka.

Ya yi alkawarin tallafa wa iyalan da aka kashe ‘yan uwansu a yayin harin, inda ya kara da cewa gwamnatinsa za ta biya dukkan diyya.

Menene ra’ayinku akan kayan sa?

Advertisement