Al'umma

Hotuna: Yadda wata mata ta cakawa mijinta wuƙa ya mutu har lahira

Kamar yadda wasu masu shiga a a kafafen yada labarai da sauran shafukan sada zumunta kamar su Facebook da Twitter suka sani, an bada rahoton wata mata ta kashe mijinta har lahira ta hanyar caka mai wuka.

Saboda muka yi kokarin kawo masu karatu cikakken labarin abin yadda ya faru har ta kashe mijinta.

Sunan matar ta Atika ƴar asalin ta yar wani kauye ne a karamar hukumar Daura ta Jihar katsinan Najeriya, suna zaune tare da mijinta a garin Mararaban Abuja da jihar Nasarawa, ita ma a Najeriya.

Advertisement

Atika da mijinta haihuwar su hudu, sai dai daya daga cikin yayan ya rasu saura uku a yanzu, mijin Atika wanda ta kashe bakaniken mota ne sunan shi Ibrahim Ahmad, kusan watanni biyar da suka wuce ya kara aure.

Haka zalika yanzu kusan shekara kenan da ya gina sabon gida wanda suka koma a ciki.

Atika ta kasance mai tsananin kishi suna yawan yin fada da mijinta game da auren da yayi na biyu, anyi mata shedar masifa sosai, kuma kafin Ibrahim ta fara yin wani aure, an ruwaito cewa shima tsohon mijinta na farko barazanar kai farmaki take yawan yi masa da wuka hakan yasa ya rabu da ita.

A baya ta ta6a yankan matar yayan mijinta da wuka a lokacin da suke fada suna gida daya kafin mijinta ya gina sabon gida su koma.

A ranar Assabar din da ta gabata 5 ga watan February, 2022 da misalin karfe 8pm na sare Ibrahim ya dawo gida kai tsaye ya wuce dakinta domin kai mata (Golden Milk) shigar shi ke da wuya a dakin sai rikici ya barke tsakanin su lamarin da ya kai su ga har ta cije shi a hannu da kirjin, shine ya fito da sauri ya nufi wajen wajen daya matar shi ta daure masa hannun.

Bayan an daure masa hannun ya juya baya yana tafiya ita kuma Atika ta sake fitowa ta zaro wuka ta biyoshi ta baya ba tare da ya sani ba ta caka mai a wuya tsakanin kafadar shi da wuyan shi, ta sake caka masa a hefen kirjin shi kusa da hammatan shi, a lokacin ne Ibraheem yace da ita kin kashe ni, kamar yadda take shedawa da kanta.

A Lokacin ne kishiyar ta tayi sauri ta shige dakin ta ta rufo kofa ta kulle kuma bata fito ba sai da ta tabbatar mutane sun shigo gidan.

Ibrahim ya fara gudu zuwa bakin kofar gida (GATE) yana Ihun neman taimako amma Atika ta sake zaro wata katuwar sanda ta bishi da gudu ta buga masa a kan shi, ta kuma buga masa har sai da kwakwalwar shi ta fito ya kama kofar (GATE) hannun shi duk jini ga kuma wuyan shi yana feshin jini, daga nan ya fadi ita kuma ta fara ihu tana cewa ta shiga uku na kashe mijina da hannu na, an dauki Ibrahim zuwa asibitin kafin a kai asibiti ya rasu.

Yanzu haka dai an yiwa Ibrahim jana’iza kamar yadda Addinin islama ya tanazar ita kuma tana hannun rundunar yan sanda ana cigaba da bincike.

Daga: M Inuwa MH

Advertisement