Al'umma

Hotuna: Minista Nwajiuba ya ziyarci IBB a Minna

Karamin Ministan Ilimi, Honarabul Chukwuemeka Nwajiuba, a ranar Litinin, ya kai wa tsohon shugaban kasa Gen. Ibrahim Babangida (Rtd) ziyarar ban girma a gidansa na Hilltop da ke Minna.

An bayyana cewa Ministan wanda ya kai ziyarar aiki jihar Neja yayi amfani da wannan ziyarar wajen ziyarar tsohon shugaban kasa kuma dattijon jihar domin tattauna halin da kasar ke ciki da kuma yadda za a tsara hanyar da za a bi.

Da yake bayyana Ministan a matsayin matashi, maras kima amma haziki, Gen. Babangida ya yabawa Hon. Nwajiuba don ziyarar.

Ya bayyana jin dadinsa da irin manyan ra’ayoyi da tunani da ke fitowa daga Ministan kan yadda za a shawo kan kalubale daban-daban da kasar ke fuskanta da kuma gina kasa mai cike da jituwa.

Advertisement