Laifuku

Hotuna: Kalli muggan makaman da aka ƙwato daga hannun ƴan daba 128 da aka cafke a Kano

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kano (PPRO), Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana a dandalin shi na sada zumunta (Facebook) a yan sa’o’i da suka gabata, inda ya bayyana fuskokin wasu daga cikin yan daba dari da ashirin da takwas (128) da aka cafke kwanan nan a jihar.

Jami’in PPRO ya bayyana cewa an damke dabar ne tsakanin da bayan bikin Sallah da aka kammala kwanan nan.

Lokacin da aka gabatar da wadannan mutanen, an kwato wasu muggan makamai daga hannun su.

Daga cikin kayayyakin da aka kwato sun hada da yankan kwalabe, adduna, wukake masu kaifi da girma daban-daban, bindiga, katafalu da almakashi. Baya ga makamai, wasu kayayyakin da aka gano sun hada da, magunguna masu sa maye da wasu kadarori da aka sace.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar (CP), Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya godewa al’ummar jihar Kano da suka tabbatar da ganin an gudanar da bukukuwan lami lafiya. Ya kuma ba da umarnin a gudanar da bincike na gaskiya kan barayin da aka kama.

Daga karshe ya yabawa gwamnatin jihar Kano, sarakunan gargajiya, malaman addini, ‘yan uwa jami’an tsaro, ‘yan banga, masu ruwa da tsaki na rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, da kungiyoyin kare hakkin jama’a (CLO) da kuma jami’an Constabulary na musamman bisa goyon baya da hadin kai da suka bayar wajen kama shi a kwanan nan. da kuma tabbatar da jihar Kano ta zaman lafiya.

Hukumar ta PPRO ta kuma tabbatar wa da jama’a cewa za a ci gaba da gudanar da sintiri tare da kai samame maboyar ‘yan ta’adda a fadin Jihar. A cewarsa, za a gudanar da hakan ne ta hanyar “Operation Puff Adder” na rundunar da ke bayar da sakamako mai kyau.

Note: Dukkan hotuna an dauke su ne daga shafin Facebook na PPRO na jihar Kano.

Back to top button