Tsaro

Hotuna: Jami’an tsaron Nijar sun kama tulin makamai a jihar Agadez

Rundunar jami’an tsaro a jamhuriyar Nijar ta samu nasarar kama wasu tulin makamai jiya Alhamis a yankin jihar Agadez.

Advertisement

Tulin makaman da jami’an tsaron suka kama a jihar sun haɗa da manyan da ƙananan bindigo. Haka zalika kuma akwai tarin alburusai masu rai (Live Ammunition) na manyan da ƙananan bindigo masu yawan gaske.

Gwamnan jihar Agadez da wasu masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro sun shaidi baje kolin makaman da aka yi a yau juma’a kamar yadda kuke gani a cikin wadannan hotuna dake kasa.

Advertisement

Wannan kamen shine babbar nasara da jami’an tsaron suka samu a kwanan nan ta fuskar yaƙi da yan ta’adda da gwamnatocin kasashen yankin Afirka ta Yamma ke yi.

Jamhuriyar Nijar ta sha fama hare-haren yan ta’adda, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane da jikkata wasu da dama, tare da mayar da dubban mutane marasa gidaje.

Wannan nasarar an same ta ne bisa namijin kokarin rundunar kiyaye zaman lafiya ta yankin jihar Agadez (Guard de national).

Advertisement