Ƙetare

HOTUNA: An Cafke Wani Tsuntsu Da Ke Hada-Hadar Miyagun Kwayoyi A Gidan Yari

Source: Sigujana_ZA

Ana amfani da dabbobi don abubuwa daban-daban da ke amfanar mutane. Sama da shekaru dubu muna ganin ana amfani da dabbobi irin su Dawakai, Giwaye, har ma da karnuka ana amfani da su wajen yaƙi don yin wasu ayyuka da mutane ba za su iya yi ba.

Har wala yau ana amfani da dabbobi wajen yin abubuwan da mutane ba za su iya ba. An dade ana amfani da tsuntsaye a matsayin manzanni, kuma ga dukkan alamu a wasu yankuna na duniya, ana amfani da tantabara wajen kai wasu sakonni zuwa wasu wurare.

Advertisement

To, akwai wasu hotuna da aka yi ta samun kulawa sosai bayan an buga su a Twitter da Facebook. Hotunan sun nuna wasu tsuntsayen da ake ganin kamar ‘yan sanda sun kama su ko kuma sun gano su, kuma abin da ya fi daukar hankali ga tsuntsayen shi ne abin da suke dauke da su, an same su dauke da kwayoyi da suke jigilar su daga wannan gidan yari zuwa wancan.

Tsuntsayen na dauke da kananan jakunkuna a kirjin su kuma kananan jakunkunan na dauke da wiwi, hodar iblis, da wasu kwayoyi. Da alama tsuntsayen sun kasance wani ɓangare na zoben miyagun ƙwayoyi na kurkuku.

Na tabbata kila kana tambayar kanka shin za a kama tsuntsaye ne ko kuma kana son sanin abin da zai faru da su, to, da yawa daga cikin mutane a cikin comments na post din suna da wasu tunanin abin da zai iya faruwa, wasu mutane, har ma suna cewa a kama tsuntsayen, yayin da wasu ke cewa kila a kashe tsuntsayen domin a hana safarar wadannan kwayoyi daga gidan yari zuwa gidan yari.

Advertisement