Tsaro

Hotuna: Ƴan bindiga sun kashe sojoji 13, ƴan sanda 5 da ƴan banga 65 a Kebbi

Wasu yan bindiga sun kashe sojoji 13 da yan sanda 5 a wani artabu da suka yi a kauyen Kanya da ke gundumar Danko-Wasagu a masarautar Zuru a jihar Kebbi.

Fadan dai ya barke a kauyen ne a ranar Talata 8 ga watan Maris, kwanaki bayan da aka yiwa kimanin yan banga 63 kisan kiyashi da ake kira Yan-Sa-Kai a Masarautar Zuru.

A cewar jaridar Punch, daruruwan yan bindiga ne suka mamaye Kanya, inda suka yi artabu da dakarun soji da na yan sanda, a wani artabu na tsawon sa’o’i uku.

Advertisement

“Mutane 19 da suka mutu sun hada da sojoji 13, yan sanda biyar da kuma ɗan banga daya,” wani jami’in tsaro da bai so a bayyana sunan shi ba,” kamar yadda majiyar tsaro da mazauna yankin suka shaida wa AFP.

Yace wasu jami’an tsaro takwas da suka hada da sojoji hudu suna kwance a asibiti da raunuka.

“An gwabza kazamin fada ne da ya dauki sama da sa’o’i uku. Ƴan ta’addan ne suka fi karfin su saboda yawan su.”

Wani mazaunin yankin, Musa Arzika, wanda ya bayar da wannan adadin, ya ce maharan sun zo ne a kan babura kusan 200 da ke hawa uku a kan kowannensu, inda suka yi wa kauyen kawanya.

“An kai gawarwakin sojoji 13, ‘yan sanda biyar da dan banga daya da aka kashe a fadan da safiyar yau zuwa Zuru. Mun yi imanin su ne ‘yan bindigar da suka kashe ‘yan banga da suka kai hari kauyen mu,” inji shi.

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya tabbatar da faruwar harin a ranar Laraba a lokacin da ya karbi bakuncin ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama a Birnin Kebbi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Duk da cewa gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar (SSG), Umar Babale Yauri, bai bada adadin sojojin da aka kashe ba, ya kara da cewa gwamnatin sa na bakin kokarinta wajen ganin ta magance matsalar rashin tsaro dake addabar yankin kudancin kasar.

“A gaskiya, kwanaki uku kacal, mun rasa ‘yan banga kusan 65. Kuma ko a jiya, mun rasa wasu jami’an soji da ke hulda da su.”

“Batun ‘yan bindiga abu ne da ba a saba gani ba a Kebbi, amma bisa la’akari da abin da ke faruwa a Zamfara, ‘yan bindigar na fuskantar babban kalubale daga sojoji, don haka suka tilasta musu shiga Kebbi musamman kudancin Kebbi.”

A martanin da Ministan ya mayar, ya ce ya je jihar ne bisa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kebbi kan kashe ‘yan banga da aka yi a jihar.

Onyeama ya ce shugaban ya bukaci jihar da ta dage wajen tunkarar kalubalen ‘yan fashin.

“Ba za a ja da baya ba kuma ba za mu daure da kalubalen ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a jihohin Arewa ba.”

Advertisement