Tsaro

Hotuna: Wasu daga cikin waɗanda suka mutu a harin jirgin ƙasa na Abuja-Kaduna [Sunaye]

A ranar 28 ga watan Maris ɗin 2022 ne wasu ƴan bindga suka dasa bam a kan hanyar da jirgin ƙasa yake wucewa daga Abuja zuwa Kaduna.

Bayan da bam ɗin ya tilasta wa jirgin tsayawa ne a ranar Litinin da daddare, sai kuma maharana suka fara harbin kan mai uwa da wabi – inda wasu bidiyo da mutane suka yaɗa a intanet suka nuna yadda wani sashe na jirgin ya yi fata-fata, da wasu gawarwaki a kwance sannan da kuma wasu da suka jikkata.

Rahotannin farko-farko sun ce fasinjoji 970 ne a cikin jirgin, amma kwana biyu bayan nan sai gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar da sanarwar cewa bayanan da ta samu daga Hukumar Kula da Jiragen kasa ta Najeriya NRC sun nuna cewa mutum 362 na a ciki.

Wasu daga mutanen da suka mutu sune;

  • Farida S Mohammed
  • Abdu Isa Kofar Mata
  • Dr Chinelo Nwando
Back to top button