Tsaro

Hizbullah ta musanta tura mayaka zuwa Ukraine don nuna goyon baya ga Rasha

Mayakan Hizbullah

Hezbollah ta Lebanon ta musanta a ranar Juma’a cewa wani daga cikin mayakanta na goyon bayan sojojin Rasha a cikin Ukraine bayan da Kyiv ya zargi kungiyar da ke samun goyon bayan Iran da kuma Syria da aika sojojin haya don tallafawa mamayar Moscow.

Babban magatakardar kungiyar Hassan Nasrallah ya bayyana a wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin cewa “Babu wani daga kungiyar Hizbullah, ko wani mayaki ko kwararre a fannin soji da ya je wannan fage ko kuma wani fage na wadannan yake-yake.”

Babban hafsan sojin kasar Ukraine ya fitar da wata sanarwa a yau Juma’a yana mai cewa kimanin sojojin hayar Siriya 1,000 da mayakan Hizbullah ne aka dauka domin yaki a Ukraine.

A cikin ‘yan kwanakin nan, shugaban Rasha Vladimir Putin ya ba da sanarwar wani shiri na ba da damar “masu sa kai” daga Gabas ta Tsakiya su shiga cikin sojojin Rasha da suka mamaye Ukraine.

Hezbollah dai na da mayaka da kwararru da ke yaki tare da gwamnatin Assad a Syria da kuma wasu a kasar Yemen da ke taimakawa Houthis.

Har ila yau, kungiyar Hizbullah tana da alaka mai karfi kuma ana kyautata zaton tana da kwararru da masu ba da shawara da ke taimakawa ‘yan ta’addar Iran da mayakan sa kai a cikin Iraki.

Advertisement