Cashew Da Rogo Na Iya Zama Haɗari Ga Lafiya

1. Cashew: Kuna iya zama masu sha’awar wannan ‘ya’yan itace mai dadi, amma ku sani cewa danyen ƙwayayen cashew na iya zama haɗari ga lafiyar ku. Ku sani Cashew da fulawa na dauke da sinadarin acid mai hatsarin gaske wanda ake kira Urushiol, wannan abu ne mai hatsarin gaske wanda yake kashe mutane idan aka sha yadda bai dace ba.

Hoto: Cashew

Urushiol ita ce acid din da ake samu a cikin gubar ivy. Akwai dogon tsari a baya wajen canja danyen cashew domin a ci.

2. Rogo: Ana cin shi a Afirka da Kudancin Amirka. A Najeriya, kabilar Ibo na son rogo musamman wanda sarrafa ta da ake kira fufu, amma yana da kyau a yi taka-tsan-tsan wajen cin rogo domin danyen rogo na dauke da sinadarin cyanogenic glycosides wanda zai iya haifar da gaggarumin matsala ko rashin lafiya ga dan Adam.

Hoto: Rogo