Ƙetare

Hatsarin Jirgin Sama Ya Laƙume Rayukan Mutane 68

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Nepal ta bayyana cewa akalla mutane 68 ne suka mutu a jiya Lahadi, lokacin da wani jirgin cikin gida ya yi hatsari a yankin Pokhara.

Muryar Amurka ta bayar da rahoton cewa, hatsarin a cewar hukumomi a kasar Nepal, shi ne hatsarin jirgin sama mafi muni cikin shekaru 30 da aka yi a karamar hukumar Himalaya.

Ma’aikatan ceto da dama na kasar Nepal na lekowa a gefen tuddan da jirgin Yeti Airlines dauke da mutane 72 daga Kathmandu babban birnin kasar ya sauka.

Advertisement

Talabijin na cikin gida ya nuna ma’aikatan ceto suna ta zagaya sassan jirgin da suka karye inda wasu daga cikin kasa da ke kusa da wurin da hadarin ya faru ya kone, tare da ganin lasar wuta.

Tashar yanar gizo ta Safety Network ta nuna cewa hatsarin shi ne mafi muni a Nepal tun shekarar 1992, lokacin da wani jirgin saman Pakistan Airbus A300 ya yi hadari a wani tsauni a kan hanyar shi ta zuwa Kathmandu, inda ya kashe dukkan mutane 167 da ke cikin shi.

Advertisement