Hatsarin Jirgin Sama Ya Kashe Mutane 62 A Ƙasar Brazil
Wani jirgin sama dauke da mutane 62 ya yi hatsari a kusa da jihar Sao Paulo a ƙasar Brazil ranar Juma’a.
Wadanda suka mutu sun hada da fasinjoji 58 da ma’aikatan jirgin hudu.
Duk da cewa tun farko ba a san abin da ya same su ba, amma a daren jiya an tabbatar da cewa dukkan mutanen 62 da ke cikin jirgin sun mutu.
Jirgin mai lamba 2283, ya fado ne a birnin Vinhedo, kamfanin da ke sarrafa jirgin, Voepass Linhas Aéreas, ya faɗa.
Jami’an yankin da ke kusa da wurin da hatsarin ya faru sun ce babu wanda ya tsira da ransa, ko da yake gida daya ne kawai a rukunin gidajen da lamarin ya faru a unguwar da hatsarin ya afku, yayin da babu wani daga cikin mazauna yankin da ya samu rauni.
Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, ya tabbatar da afkuwar hatsarin a yayin da yake magana a wani lamari da ya faru jim kadan bayan hadarin.
“Dole ne in kasance mai ɗaukar mummunan labari,” in ji shugaban, yana jaddada gaskiyar hadarin tare da neman shiru na minti daya ga wadanda abin ya shafa.
Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Voepass ya ce jirgin wanda ya taso daga Cascavel a jihar Parana, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa babban filin tashi da saukar jiragen sama na Sao Paulo, ya fado ne a Vinhedo, wani gari mai tazarar kilomita 80 daga arewa maso yammacin Sao Paulo.
Radar irgin ta mai binciken jirgin FlightRadar24 a matsayin turboprop ATR 72-500.