Labarai

Harin Wata Ƙungiya Mai Alaƙa Da Al-Qaeda A Mali Ya Kashe Mutane Fiye Da 70

Sama da mutane 70 ne ake tunanin an kashe a wani hari da wata kungiya mai alaka da al-Qaeda ta kai Bamako babban birnin kasar Mali a farkon wannan mako, kamar yadda majiyoyin diflomasiyya da na tsaro suka bayyana.

Mayakan kungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wa al-Muslimeen (JNIM) sun kai harin ne a wata makarantar horas da ‘yan sanda da ke kusa da filin tashi da saukar jiragen sama a ranar Talata, lamarin da ya haifar da kaduwa da fusata a wannan kasa ta yammacin Afirka.

Saboda tsaro, majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutane 77 ne suka mutu yayin da 255 suka jikkata a harin.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya kara da cewa, wata sahihiyar takarda ta sirri ta ce adadin wadanda suka mutu ya kai kusan 100, inda aka gano mutane 81 da abin ya shafa.

Jami’an diflomasiyya biyu da ke aiki a yankin, ciki har da daya da ke Bamako, sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa adadin wadanda suka mutu ya kai shekaru 70.