Tsaro

Harin Rasha a tsohon babban birnin Ukraine, ya kashe mutane 11 duk da tattaunawar zaman lafiyar da ake yi

Harin na Rasha ya kashe fararen hula akalla 11 a birnin Kharkiv na biyu mafi yawan jama’a a ranar Litinin, gwamnan yankin ya kara da cewa wasu da dama sun jikkata.

Advertisement

Harin na zuwa ne a rana ta biyar da farmakin da Rasha ke kaiwa Ukraine kuma kwana daya bayan da sojojin Ukraine suka dakile wani hari da sojojin Moscow suka kai a birnin Kharkiv.

Oleg Sinegebov, ya rubuta a cikin manhajar saƙon Telegram cewa, “Maƙiyan Rasha suna jefa bama-bamai a wuraren zama na Kharkiv, inda babu muhimman ababen more rayuwa, inda babu wani matsayi na sojoji.”

Advertisement

“Sakamakon hare-haren bama-bamai da ke gudana, ba za mu iya yin kira ga jami’an agajin gaggawa ba, a halin yanzu akwai mutane 11 da suka mutu da dama kuma suka jikkata,” in ji shi.

Fadar Kremlin ta fada jiya litinin cewa babban aikin sojin Rasha shine tabbatar da tsaron fararen hula.

Sai dai Rasha ta kuma zargi kungiyoyin ‘yan kishin kasa a Ukraine da yin amfani da fararen hula a matsayin garkuwa da kuma sojojin Ukraine da jibge manyan makamai zuwa wuraren zama, a matsayin hujjar da ke tabbatar da mutuwar fararen hula.

AFP

Advertisement