Tsaro

Hare-haren yan tawaye sun kashe sojojin Jamhuriyar Congo fiye da 20

Sama da sojojin Congo 20 ne aka kashe a wani hari da kungiyar ‘yan tawayen M23 ta kai a wani sansanin soji a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC), kamar yadda wasu majiyoyi na cikin gida suka bayyana, kamar yadda gidan talabijin na Alzajeera ya wallafa.

An kaddamar da harin ne a daren ranar Litinin a Nyesisi dake lardin Kivu ta Arewa kusa da gandun dajin Virunga, wani wurin tarihi na UNESCO dake dauke da gorilla (Gwaggon Birai) masu hadari.

Ana cigaba da gwabza fada a ranar Laraba, a cewar majiyoyin kungiyoyin fararen hula da na kananan hukumomi.

Advertisement

Dakarun Congo da aka fi sani da FARDC ba su tabbatar da asarar rayuka ba, haka ma jami’an agaji ba su tabbatar da samun isa wurin da fadan ya yi ba.

Gentil Karabukala shugaban kungiyoyin farar hula na Kisigari dake kusa da Nyesisi yace an kashe sojoji 29 a harin.

Laftanar Kanar Muhindo Lwanzo, babban hafsan hafsoshi na yankin Rutshuru, yace daya daga cikin sojojin da aka kashe Kanal ne.

Lwanzo ya kara da cewa yan tawayen sun kuma samu raunuka, ba tare da bayar da adadi ba.

Advertisement