Tsaro

Hanifa Abubakar: Kotu ta bada umarnin sakin Jamila matar Abdulmalik Tanko

Wata kotun Majistrate dake da zamanta a Jihar Kano ta bada umarnin sakin Jamila, matar Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar su Hanifa Abubakar wanda ake zargi da sacewa tare da kisan ta.

Idan dai za’a iya tunawa, ana zargin Jamila ne da laifin haɗa baki da mijinta Tanko wajen yin garkuwa da Hanifa da kuma kashe ta a kwanakin baya, zargin da matar ta musanta ranar Alhamis lokacin da ta bayyana a kotun ta Magistrate a Kano.

Mai magana da yawun kotunan Jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya shaidawa sashen Hausa na BBC cewa kotun ta bada umarnin a sake ta ne bayan ta yi nasarar wanke kanta daga zarge-zargen ake tuhumar ta da su a gaban kotun, waɗanda suka haɗa da haɗin baki.

Advertisement

Ibrahim ya ƙara da cewa masu shigar da ƙara a ma’aikatar shari’a ta Jihar Kano sun amince su yi amfani da ita a matsayin shaida a kan mijinta Abdulmalik Tanko, inda za ta sake komawa kotun don bayyana abubuwan da ta sani game da wanda ake zargin (Mijinta).

Advertisement