Al'umma

Gwamnonin Arewa ta Tsakiya sun koka da karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, kuma shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa ta tsakiya (NCSGF), ya koka da yadda ake samun karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta sakamakon kalubalen tsaro da ke addabar jihar da wasu sassan kasar nan.

Bello ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da yakin neman zabe na shiyyar Arewa ta tsakiya a shekarar 2022 kan yaran da ba su zuwa makaranta a Minna.

Ya ce zai yi wuya a shawo kan iyaye su saki ‘ya’yansu ko unguwanni don zuwa makaranta.

Advertisement

Ya ce, “Ba shakka, a duk inda ake rashin tsaro, ba ka tsammanin iyaye za su bar ‘ya’yansu su tafi makaranta musamman a yanayin da ake sace su don neman kudin fansa.”

Bello ya bayyana cewa, babu wani ci gaba mai ma’ana a fannin ilimi da za a samu, sai dai in an tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce, “Muna bukatar mu kara himma wajen magance matsalolin tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummarmu, domin idan ba su da tsaro, zai yi wuya a shawo kansu su fita zuwa makaranta.

Yayin da muke kokarin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, ya kamata mu kara himma wajen ganin mun samar da tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi. Yin hakan zai ba da damar samun ci gaba cikin sauri a fannin ilimi.

A nasa jawabin karamin ministan ilimi Mista Chukwuemeka Nwajuiba, ya bayyana cewa ma’aikatar na yin cudanya da gwamnatin jihar Neja domin ganin an fitar da yara kan tituna an dawo da su makaranta.

Ya ce ma’aikatar ta yi nazari a kan ayyukan da jihar ta yi a fannin ilimi a cikin shekaru bakwai da suka gabata, inda ya tabbatar da cewa an samu ci gaba sosai wajen shiga makarantu.

Kwamishinan ilimi na jihar kuma shugaban ilimin bai daya na jihar Neja, Dakta Isah Adamu ya jaddada kudirin jihar na rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Ya ce tare da taimakon gwamnonin jihohin Arewa da sauran masu ruwa da tsaki, jihar ta yi nasarar rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta daga 513,963 zuwa 298,192.

Advertisement