Siyasa

Gwamnonin APC 2 Da Suka Yi Kukan Cewa Yan Ta’adda Sun Mamaye Jihohinsu

Hoto: Domin misali da yan ta’adda

Yan bindiga da yanzu haka aka fi sani da yan ta’adda a Najeriya na cigaba da haddasa asarar rayuka da dukiyoyi ta hanyar hare-haren da suke kai wa a wasu jihohi musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Kafin yanzu dai yan ta’addar Boko Haram ne suka firgita da ta’addanci. Sai dai kuma ga dukkan alamu ‘yan bindigar da ke dauke da makamai ne suka ja-gaba a yayin da jahohin da abin ya shafa da mazauna yankin ke rayuwa cikin fargabar ‘yan ta’adda.

A kwanakin baya ne wasu gwamnoni biyu da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC mai mulki suka yi kukan cewa ‘yan ta’adda sun mamaye jihohinsu.

Advertisement

(1). Gwamna Babagana Zulum (Jihar Borno).

A da Borno ce ta fi fama da matsalar Boko Haram. Yayin da ake ganin yana raguwa saboda ayyukan soji a jihar, hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa da alama ya kara dagula al’amura.

Yanzu da aka sanya ‘yan fashi da makami su ma a matsayin ‘yan ta’adda, hakan na nufin an yi musu lakabi da makiyan kasa. Zulum ya koka da yadda wasu kananan hukumomi biyu a Borno: Abadam da Guzamala ke karkashin ikon ‘yan ta’addar Boko Haram. Ya kuma yi kira da a taimaka wa gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro duk da cewa ayyukan ‘yan fashin na karuwa.

(2). Gwamna Bello Matawalle (Jahar Zamfara).

Jihar Zamfara ce ta fi fama da matsalar a lokacin da ake maganar hare-haren ‘yan bindiga. Hare-haren da suke kai wa a Zamfara yana karuwa tun kafin a ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

A cewar Matawalle, jihar a halin yanzu tana da sama da mutane 600,000 a sansanin ‘yan gudun hijira na cikin gida (IDPs).

Yawancin mutanen da aka lalata gidajensu ko kuma wadanda suka gudu daga gidajensu don gujewa hare-hare da kashe-kashen da ‘yan bindiga ke yi. Matawalle ya yi zargin cewa ana sakin wasu ‘yan bindiga da aka kama ba tare da an hukunta su ba, kuma hakan ya kara musu kwarin gwiwar cigaba da mulkin ta’addanci a Zamfara da sauran jihohin.

Idan dai za a iya tunawa ‘yan bindiga sun kashe wasu mutane a Zamfara a makon jiya. Kawo yanzu dai babu wani da aka kama ko gurfanar da shi a gaban kotu duk da cewa Gwamna Matawalle na cigaba da zargin ana tafka magudi wajen gurfanar da ‘yan ta’addan a gaban kuliya.

Advertisement