Siyasa

Gwamnoni Ba Su Adawa Da Zaben Fidda Gwani Na Kai Tsaye – Gwamna Abdullahi Sule

Hoto: Gwamna Abdullahi Sule Nasarawa

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, a ranar Lahadin da ta gabata ya yi watsi da ikirarin da wasu bangarori da dama ke yi na cewa gwamnonin jihohi na adawa da amincewa da zaben fidda gwani da jam’iyyu suka yi a cikin dokar gyara dokar zabe.

Sule, wanda ya bayyana hakan a wani taro da aka yi a birnin tarayya kan dokar zabe, ya bayyana sarai cewa gwamnonin ba sa adawa da zaben fidda gwanin kai tsaye.

Majalisar dokokin kasar ta zartar da kudirin dokar zabe a ranar 9 ga Nuwamba, 2021 kuma ta amince da zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasa a kasar.

Advertisement

Yan majalisar sun kuma amince da watsa sakamakon zabe a Najeriya ta hanyar fasahar zamani, wato ta hanyar intanet.

A watan Disambar shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da sanya hannu kan dokar zabe kan batun zabukan fidda gwani da sauran batutuwan da ke cike da cece-kuce a cikin takardar.

Gwamnan yace: “Akwai rashin fahimtar cewa gwamnonin na adawa da zaben fidda gwanin kai tsaye. Tabbas gwamnonin ba sa adawa da zaben fidda gwani na kai tsaye. A gaskiya ma, yawancin jihohi sun zaɓi yin kai tsaye ko a kaikaice.

“Ba wai gwamnonin jihohi suna adawa da kai tsaye ba. Abin da muka ce shi ne me yasa ba za ku bar jam’iyyu su bi hanyar da suke so ba. Dokar zabe ta wuce kai tsaye ko kai kaikaice. Akwai muhimman abubuwa da yawa a ciki, me yasa muke damben kanmu da zaben kai tsaye ko a kaikaice?

“A bawa jam’iyyun siyasa dama. A lokacin da aka bada dama, za ku yi mamaki a zaben 2023, yawancin jihohi za su yi kai tsaye.”

Advertisement