Siyasa

‘Gwamnoni 14 sun amince da takarar shugaban kasar Tinubu’ – Inji Jibrin

Bola Tinubu

Darakta-Janar na kungiyar goyon bayan Bola Ahmed Tinubu, Abdulmumin Jibrin, ya ce a ranar Juma’a akalla gwamnonin jihohi 14 ne suka bayyana goyon bayansu ga burin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a 2023.

Advertisement

Jibrin, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, ya kara da cewa shugabannin jam’iyyar APC na jihar 26 sun kuma amince da takarar tsohon gwamnan jihar Legas.

Sai dai ya ki bayyana sunayen gwamnoni ko shugabannin jam’iyyar da suka bayyana goyon bayansu ga Tinubu

Advertisement

Jubrin dai tsohon dan majalisar wakilan Najeriya ne.

Abinn da rubuta: “Gwamnoni 14 sun shiga kuma 4 suna tattaunawa. Shugabannin jihohi 26 a cikin. Ba za mu kai hari ko hana kowa takara ba.

“Muna amfani da ‘yancin zabin mu ta hanyar tallata Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Za mu kasance masu alheri kuma kofofin mu a buɗe yanzu da kuma bayan nasarorin mu. “

Tsohon gwamnan jihar Legas ya tabbatar da aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar mafi girma a siyasar kasar a watan jiya a fadar shugaban kasa.

Advertisement