Labarai

Gwamnatin Ta Dawo Da Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamiɗo Kan Sarauta

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da sake nada Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano bisa sabbin dokoki.

Gwamnan ya baiwa tsofaffin sarakuna wa’adin sa’o’i 48 da su bar fadarsu tare da mika kadarori na masarautun ga kwamishinan kananan hukumomi, wanda kuma yake rike da mukamin mataimakin gwamnan jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rattaba hannu a kan kudirin dokar Masarautar Kano na shekarar 2024, inda ya soke dokar masarautun 2019 wadda ta sauya tarihin jihar na sama da shekaru 1000.

Da sanya hannu kan dokar, gwamnan ya bayyana cewa an soke dokar 2019 kuma yanzu ta zama tarihi.

Rattaba hannun ya samu halartar shugaban majalisar dokokin jihar Ismaila Falgore da mataimakin gwamna Aminu Abdussalam da sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Baffa Bichi da sauran su.

Majalisar dokokin jihar ta cika daya daga cikin ayyukanta na tsarin mulki ta hanyar sanya hannu kan kudirin ya zama doka.

Advertisement