Al'umma

Gwamnatin Swaziland ta umurci maza da su auri mata 5 ko su tare a gidan yari

Shugaban kasar Switzerland

Sarkin Swaziland, Sarki Mswati III ya bayyana a kasar cewa mazaje sun auri akalla mata biyar ko kuma su shiga gidan yari.

Sanarwar da Sarkin ya fitar ta kafafen yada labarai ya yi kira ga dukkan mazan kasar da su auri akalla mata biyar, inda ya ba su tabbacin cewa gwamnati za ta biya kudin daurin auren tare da siya musu gidaje.

“Ga yarjejeniyar, auri akalla mata biyar kuma an tabbatar muku da cewa gwamnati za ta biya kudin daurin auren kuma ta saya musu gidaje.”

Advertisement

Sarki Mswati ya yi gargadin cewa duk mace ko namiji da suka yi adawa da shawarar “za su fuskanci hukuncin daurin rai da rai”.

Dokar dai ita ce a tabbatar da kowace mace ta samu miji domin ana kyautata zaton mazan da ke kara auren zai taimaka wa mata wajen samun mazaje.

Sarkin ya bayyana cewa akwai mata fiye da maza a Swaziland wanda ya ce babbar matsala ce ga kasar da aka san tana da budurwowi.

Rahotanni sun ce an kuma yanke hukuncin ne biyo bayan karuwar budurwowi da karancin maza a kasar.

Shi kansa Sarki Mswati yana da mata 15 da ’ya’ya 25, yayin da mahaifinsa da magajinsa ke da mata sama da 70 da ‘ya’ya sama da 150.

Advertisement