Tsaro

Gwamnatin Najeriya ta amince da bukatar Amurka na mika mata Abba Kyari

Gwamnatin Tarayya Najeriya ta amince da bukatar kasar Amurka na mika mata kwamandan rundunar yan sandan dake ba da ga bayanan sirri da aka dakatar, mataimakin kwamishinan yan sanda, DCP Abba Kyari.

Amurka ta bukaci a mika mata Kyari bisa zargin damfarar dala miliyan $1.1 na waya da Abass Ramon aka Hushpuppi da wasu mutane hudu suka yi.

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) ne ya bayyana haka a wata takardar da ya shigar gaban babban alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A cikin takardar da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022, kuma aka shigar a karkashin dokar karewa, Malami yace bukatar da wakilin diflomasiyya na ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya bukata ne.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa wakilin FBI na musamman Andrew Innocenti, yayi zargin cewa Hushpuppi ya kulla yarjejeniya da Kyari ne bayan wani “mai hada baki,” Chibuzo Vincent, ya yi barazanar fallasa zargin damfarar $1.1m da aka yi wa wani dan kasuwa dan kasar Qatar.

Innocenti, wanda yace ya samu kiran waya da tattaunawa ta WhatsApp tsakanin Kyari da Hushpuppi, ya kuma yi zargin cewa dan sandan ya biya N8m ko $20,600 domin kama Vincent da tsare shi.

Ofishin mai shigar da kara na Amurka da ke tsakiyar gundumar California ta umurci FBI da ta kama Kyari kusan shekara guda da ta wuce.

Kyari ya shiga shafin Facebook a ranar 29 ga Yuli, 2021, don musanta zargin, amma daga baya ya goge sakon bayan ya gyara shi kusan sau 12.

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya bayar da shawarar dakatar da Kyari, wanda hukumar ‘yan sandan ta aiwatar a ranar 31 ga Yuli, 2021.

A ranar 2 ga watan Agustan 2021 ne shugaban ‘yan sandan ya kafa kwamitin bincike na musamman karkashin jagorancin mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar, Joseph Egbunike, domin gudanar da bincike kan zargin.

An mika sakamakon binciken kwamitin zuwa ofishin AGF wanda ke da alhakin al’amuran da suka shafi mayar da su gida da kuma mika wadanda ake zargi ko wadanda ake nema ruwa a jallo.

A ranar Alhamis, AGF ta ce laifin da aka nemi a mika Kyari “ba siyasa ba ne kuma ba karamin abu ba ne”.

Back to top button