Tsaro

‘Gwamnatin Mafia’ ta Amurka ita ce ta ƙirƙiri rikicin Ukraine – Khamenei

Iran na fatan kawo karshen yakin da ake yi a Ukraine amma ta yi imanin cewa rikicin ya samo asali ne daga manufofin Amurka da sauran kasashen yammacin duniya, inji shugaban kolin Iran Ayatollah Ali Khamenei.

“A Ukraine, muna goyon bayan dakatar da yakin,” inji shi yayin jawabin da aka yi ta gidan talabijin a ranar Talata, ya kara da cewa za’a iya magance rikicin ne kawai idan an san “tushen” wanda ya bayyana a matsayin manufofin kasashen yammacin Turai.

Khamenei ya ce “mulkin mafia” na Amurka yana haifar da rikice-rikice da dama a duniya, wadanda ya ce sun hada da kirkiro kungiyar ISIL (ISIS), da tsoma baki cikin harkokin wasu kasashe ta hanyar tilasta sauye-sauyen gwamnati da kafa ‘yan siyasa masu goyon bayan Yamma.

Advertisement

Ukraine ta fada cikin “wanda aka zalunta” ga irin wadannan manufofin kuma an jawo ta zuwa halin da take ciki, in ji babban shugaban.

Advertisement