Al'umma

Gwamnatin Katsina Ta Tsige Wani Basarake Kan Alaka Da Yan Ta’adda

Majalisar Masarautar Katsina ta tabbatar da korar wani hakimi mai suna Makaman Katsina, Idris Sulefor, bisa zargin shi da taimakawa ta’addanci a yankin shi, inji rahoton Premium Times.

Advertisement

A wata wasika da PREMIUM TIMES ta gani mai dauke da kwanan wata 19 ga watan Junairu, 2023, Kauran Katsina, wanda shi ne Hakimin Rimi, Aminu Nuhu – Abdulkadir, ya ce an kori Makama ne bayan da kwamitin gwamnatin jihar ya same shi da laifin tuhume-tuhumen da mutanen shi suka yi masa.

“Bayan wasikar da majalisar masarautar ta samu daga ofishin sakataren gwamnatin jihar mai lamba SEC/54/Vol. VI/1416, wanda gwamnan zartarwa ya tabbatar da cewa zargin da ake yi maka gaskiya ne. Batutuwan da aka taso akan ka sun haifar da wargaza zaman lafiya a yankin ka. Don haka majalisar masarautar tana son sanar da kai cewa an sauke ka daga mukamin ka na Makaman Katsina, hakimin Bakori,” in ji Mista Abdulkadir, wanda shi ne babban Sarki a masarautar.

Advertisement

Mai magana da yawun Masarautar, Ibrahim Bindawa, ya tabbatar da sallamar ga jaridar ta yanar gizo.

Korarre Makaman Katsina ya shiga jerin sunayen sarakunan Arewa maso Yamma da aka kora bisa zargin shi da alaka da ‘yan ta’adda da suka shafe sama da shekaru goma suna tada zaune tsaye.

Aikin ta’addanci ya yi sanadiyar mutuwar miliyoyin mutane tare da raba su da muhallan su.

Advertisement