Al'umma

Video: Gwamnatin Kano ta Umarci Asadus-sunnah ya janye barazanar kisa ga Nafisa

Kwamishinan addini na Jahar Kano ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje Dr. Tahir Baba Impossible yayi bayani a madadin gwamnatin Kano cewa hankalin gwamnatin Kano ya tashi matuƙa dataji wani malami yana cewa suna da ƴan daba daza su tura suyi kisa.

Advertisement

Yace gwamnatin Kano ta saurari dukkan ɓangarorin uku tun da farko Sheikh Daurawa yayi kuskure domin jawaban sa cike suke da kuskure da bai kamata ace malami yazaɓi irin wannan salo don isar da da’awa ba ace malami yana amfani da kalamai na batsa ko waɗanda zasu riƙa tayar da ƙura ko alamun cin zarafi ga wani jinsi ba.

Baba Impossible yace gwamnatin Kano ta kuma saurari yarinyar kuma tayi kuskure maganar abun daya shafi malamai bai kamata ta tsoma baki ba tana matar Aure ko bazawara ko kuma budurwa, hakanan jawaban yarinyar dukda ba zagi bane ƙarara amma sunyi muni matuƙa ya kamata ta kiyaye.

Advertisement

Baba Impossible yace hankalin gwamnatin Kano ya tashi matuƙar gaske da taji daga cikin masu martani kan dan barwar wani malami yana cewa suna da ƴan daba daza su tura a kashe, kuma sai gwamnatin Kano ta lura a media akwai masu kwament da bidiyo suna cewa zasu kashe yarinyar ko suyi mata fyaɗe ,

Gwamnatin Kano tana kira ga wannan malami mai barazanar kisa yafito ya janye kalaman sa haka nan duk wani dayasan yayi barazanar yin wani abu a media yafito ya janye don gwamnatin Kano tuni ta watsa jami’an ta suna monitoring social media akan batun kuma sun tattara bayanan mutane sosai sun ajiye aduk sanda aka ce wani abu ya faru to gwamnatin Kano zata tuhume su kuma gwamnatin Kano na sanya idanu aduk wani motsi da sukeyi inji Dr. Tahir Baba Impossible kwamishinan Addini a jahar Kano.

Yace gwamnati bata yarda da ɗaukar doka a hannu ba idan wani ya aikata laifi a kaiwa ƴan sanda report suza su kama mai laifin su hukunta shi.

Advertisement