Al'umma

Gwamnatin Kano ta dakatar da lasisin makarantu masu zaman kansu

Hanifa Abubakar

A ranar Litinin din da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano ta dakatar da lasisin makarantu masu zaman kansu kan kisan da aka yi wa Hanifa Abubakar.

Gwamnatin jihar Kano ta ce an dakatar da lasisin makarantun har sai an tantance su.

Kwamishinan Ilimi Sanusi Said Kiru ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai.

Advertisement

Dukkanmu muna sane da yadda ake ci gaba da shari’ar mutuwar Hanifa domin wani wanda ake zargi mai suna Abdulmalik Tanko wanda shi ne mamallakin makarantar Noble Kids Academy ya yi mata kisan gilla, kuma bisa la’akari da abin bakin ciki da ya faru, musamman dangane da yadda aka kashe ta a makarantar mai zaman kanta, gwamnatin jihar ta yanke shawarar janye satifiket na duk wasu makarantu masu zaman kansu domin a sabunta su,” in ji Kiru.

Dakatarwar ta zo ne kwanaki bayan da maigidan makarantar Noble Kids Abdulmalik Tanko ya amsa laifin kashe Hanifa Abubakar ‘yar shekaru biyar a makarantarsa.

Kwamishinan ilimi ya ce za a kafa kwamiti na musamman da zai tantance makarantun tare da fitar da matakan da za a yi amfani da su wajen amincewa da lasisin makarantu masu zaman kansu a jihar.

Ya kuma ce duk makarantun da ba su cika sabbin sharuddan ba, ba za a sake bude su ba.

Advertisement