Tsaro

Gwamnatin Burkina Faso ta musanta cewa sojojin kasar sun kwace ikon kasar

Gwamnatin Burkina Faso ta ce sojojin kasar ba su karbe ikon kasar ba a ranar Lahadi ba, bayan da aka yi musayar wuta a wasu barikokin sojoji, ciki har da biyu a babban birnin kasar, Ouagadougou.

Advertisement

Wani dan jarida na Reuters ya ce, an fara luguden wuta mai tsanani a sansanin Sangoule Lamizana na babban birnin kasar, wanda ke dauke da babban hafsan sojojin kasar da kuma gidan yari wanda fursunonin da suka hada da sojoji da ke da hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekarar 2015, ta fara ne da misalin karfe 5:00 na safe (0500 GMT).

Daga baya dan jaridar ya ga sojoji suna harbin iska a sansanin. Wani ganau ya kuma bayar da rahoton harbin bindiga a wani sansanin soji da ke Kaya mai tazarar kilomita 100 daga arewacin Ouagadougou.

Advertisement

“Bayanan da ake samu a shafukan sada zumunta za su sa mutane su yi imani da cewa sojoji sun kwace,” in ji kakakin gwamnati Alkassoum Maiga a wata sanarwa a ranar Lahadi.

Gwamnati, yayin da ta fahimci sahihancin harbe-harbe a wasu bariki, ta musanta wannan labarin, ta kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu.”

Rikicin ya zo ne kwana guda bayan arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zanga a lokacin zanga-zangar adawa da gazawar hukumomi wajen dakile tashe-tashen hankula da suka addabi kasar da ke yammacin Afirka.

Advertisement