Al'umma

Gwamnatin Algeria zata fara biyan $100 ga matasa marasa aikin yi duk wata kafin su samu aiki

Shugaban kasar Algeriya ya bayyana hakan ne a ranar Talata ta hanyar watsa shirye-shiryen gidan talabijin na kasar, inda ya ce za’a fara biyan kudaden ne a watan Maris ga masu neman aiki masu shekaru tsakanin 19 zuwa 40.

A cewar shugaban, an dauki matakin ne domin kiyaye “ martabar matasa.

Ya kara da cewa akwai sama da matasa 600,000 da ba su da aikin yi a Aljeriya wanda kashi 15 cikin 100 na al’ummar kasar yana da muhimmanci a yi wani abu.

Advertisement

Sanarwar na zuwa ne watanni uku bayan da yan majalisar dokokin kasar suka kada kuri’ar soke tallafin da jihohi ke ba da kayayyakin yau da kullun.

Ga matasan da suka cancanta, za su iya karbar kusan dala $100 (£ 73) a wata ko kuma Naira ₦41,500, da kuma wasu fa’idodin jinya har sai sun sami aiki.

Izinin yayi daidai da kusan kashi biyu bisa uku mafi ƙarancin albashi na dinari 20,000 ($142)

Bugu da kari, za a dakatar da haraji kan kayayyakin masarufi ga masu cin gajiyar.

Da yake sanar da hakan, Mista Tebboune yace Aljeriya ita ce kasa ta farko a wajen Turai da ta bullo da irin wannan fa’ida.

Advertisement