Gwamnati Ta Bada Umurnin Sakin Ton 102,000 Na Shinkafa Da Masara
Matsalar karancin abinci da ake fama da ita a kasar, hade da hauhawar farashin kayayyaki yasa gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bada umarnin sakin shinkafa da masara ton 102,000 ga ‘yan Najeriya.
Gwamnati ta kuma bayyana cewa za ta iya shigo da duk wani gibi da za a iya samu don kara kayan masarufi.
Mohammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron kwamitin shugaban kasa kan bada agajin gaggawa na abinci, wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa, Abuja, ranar Alhamis.
Ya ce shugaban kasar ya bada umarnin cewa “za a samar da abinci, duk abin da ake bukata.”
Matakin dai ya biyo bayan zaman tattaunawa da kwamitin ya yi, dangane da zanga-zangar da ‘yan Najeriya suka yi kan tsadar abinci da sauran kalubalen tattalin arziki.