Tsaro

Gwamnan Benue ya zargi gwamnatin Buhari da aiki tare da ƴan bindiga, Boko Haram

A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya caccaki gwamnatin tarayya kan tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Advertisement

Gwamnan ya kaddamar da hare-hare da dama kan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan rashin tsaro, tattalin arziki da sauran manyan batutuwan kasa tun shekarar da ta gabata.

Ortom, ya yi jawabi ga tawagar jami’an gudanarwa na Kwalejin Gudanarwa ta Najeriya (ASCON) karkashin jagorancin Darakta Janar na Hukumar, Misis Cecilia Gayya a gidan gwamnati da ke Makurdi, ya bukaci yan Najeriya da su dora wa gwamnatin tarayya alhakin kashe-kashen da yan Boko Haram, yan fashi da makiyaya ke yi a kasar.

Advertisement

Ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Buhari da aiki tare da ƴan ta’adda.

Gwamnan yace: “Matsalar rashin tsaro a Najeriya a yau na mutum ne ya haddasa ta. Gwamnatin tarayya ta yanzu ce ke da alhakin kashe-kashe saboda na dauki matakai tun daga 2016 da na zama gwamna na ga wannan matsalar tana zuwa. Kuma a yau ina gargadin yan Najeriya, wadanda suke zaune a wuraren su, ina so su gane.

A makon da ya gabata ne wani abokin aikina a yankin Arewa maso Gabas ya yi kira da a ce kungiyar ISWAP ta karbe wani bangare na jihar shi kuma a hankali suna shigowa, suna na kisa kuma za su iya mamaye kasar nan bisa ga abin da ya gani. Kuma na yarda da shi cewa idan ba mu yi hankali ba, hakan zai iya faruwa.

Kamar yadda na yi tsokaci a baya game da kalubalen da muke fuskanta cewa idan ba mu yi hankali ba, wata rana abin da ya faru a Afghanistan, Allah ya kiyaye, zai iya faruwa a Najeriya. Kuma zai bayyana a gare ni cewa wannan wannan gwamnati tana son mika Najeriya ga yan ta’adda. Wannan mataki da rashin daukar matakan da suke yi ya tabbatar min da cewa suna aiki da ya ta’adda. Gaskiyar kenan, inji Ortom.

Advertisement