Siyasa

Gwamnan Adamawa ya musanta jita-jitar sauya sheka daga PDP zuwa APC

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa yana shirin sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Fintiri ya ci gaba da cewa shi mutumin PDP ne kuma ba shi da niyyar barin wata jam’iyyar.

Fintiri ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis ta bakin Mista Solomon Kumangar, Daraktan sa na yada labarai da sadarwa yayin da yake mayar da martani game da jita-jitar da ta taso daga maganganun da kafofin sada zumunta suka yi daga masu kaunar APC suna cewa Fintiri ba da dadewa ba zai sauya sheka zuwa APC.

A cikin wata sanarwa da Solomon Kumangar ya fitar ya jaddada cewa gwamnan baya tunanin barin jam’iyyar ta PDP, amma a hankali yake jagorantar jam’iyyar a jihar ta Adamawa don cimma nasarar ci gaban mutane.

A cewar sanarwar, “Ya ci gaba da mai da hankali kan aikin samar da shugabanci na gari ga dukkan sassan jihar.”

An yaudari cewa Gwamna Ahmadu Fintiri ya tafi Abuja don neman mambobin jam’iyyar APC, amma sanarwar da ta fito daga gidan Gwamnati da ke Yola wacce ta ce ba al’adar gwamnati ba ce ta shiga batutuwa da ‘yan adawa “jarumai a kafofin sada zumunta”.

Dangane da mayar da hankali kan alakar siyasa, sanarwar ta ce, “Abin da ya fi muhimmanci a wannan lokacin shi ne ‘yan Najeriya na kowane bangare na rayuwa su hada karfi da karfe su shawo kan kalubalen da ke fuskantar kasar.”

Back to top button