Al'umma

Gwamna Ortom ya ba da umarnin a yi bincike kan gonar Obasanjo da aka kona a Benue

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan kona wata gona a jihar, mallakar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Wasu da ake kyautata zaton sun kona gonakin mangwaro ne da ke Howe a karamar hukumar Gwer ta jihar Binuwai, sun kona gonar mangwaro a karshen makon da ya gabata.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran sa, Nathaniel Ikyur, Ortom ya bayyana bakin cikinsa kan lamarin, yana mai tabbatar da hakan a matsayin “aikin zagon kasa”.

Advertisement

“Saboda haka ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin don gano musabbabin barkewar gobarar,” in ji sanarwar.

Gwamnan ya jaddada cewa, ba za a amince da wani aiki na zagon kasa a jihar ba musamman ganin cewa gwamnatinsa na da manufar karfafa gwiwar masu zuba jari na gida da na waje musamman a harkar noma.

An ambato gwamnan kamar haka; “Ya zama kololuwar rashin da’a ga kowa ya yi tunanin kona wata gona da aka shirya, nan gaba kadan, za ta bunkasa tattalin arzikin yankin musamman da ma jihar baki daya.

“Obasanjo a matsayinsa na tsohon shugaban kasa dan jiha ne kuma yana bukatar a girmama shi a duk inda yake a Najeriya da kuma jihar Benue ba za a iya ware shi ba.”

Don haka ya umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar Binuwai da ya tabbatar da cewa an kama wadanda suka aikata laifin nan take kuma a gurfanar da su a gaban kotu.

Advertisement