Al'umma

Gwamna Ganduje Ya ƙarbi Kalangun gargajiya a matsayin karramawa [Hotuna]

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR ya karbi lambar yabo daga shugaban tsangayar nazarin zamantakewar al’umma inda ya samu digirin digirgir na PHD a fannin harkokin gwamnati tsakanin shekarar 1989 zuwa 1993.

Advertisement

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wata lacca mai taken “Kalubalan Rashin Tsaro da Gina Kasa” a taron kungiyar tsofaffin daliban Jami’ar Ibadan na shekarar 2022.

An tattaro cewa kungiyar tsofaffin daliban jami’ar Ibadan ce ta shirya laccar a dakin taro na Dame Okowa, Dr. Michael Omolaye Alumni Complex Jami’ar Ibadan, jihar Oyo.

Advertisement

Haka kuma gwamnan ya aza harsashin gini mai ɗaukar mutum 500 da ya gabatar wa Abdullahi Umar Ganduje lakcature dakin taro na tsangayar ilimin likitanci na jami’ar Ibadan.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Honorabul kwamishinoni da ‘yan majalisar zartarwa ta jihar Kano, wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Kano, ‘yan majalisar wakilai, shugabannin manyan makarantu, na kananan hukumomi. Shuwagabannin Gwamnati, Shugabannin Jam’iyya da Dattawa, ‘Yan Kasuwa, da Sauransu.

Advertisement