Wasanni

Granada ta kori kocin ta Moreno

Granada ta kori kocim kungiyar Robert Moreno bayan buga wasanni tara ba tare da samun nasara ba ya bar kungiyar a matsayi daya a saman teburin gasar La Liga.

Advertisement

Kungiyar ta fitar da takaitaccen bayani a ranar Lahadi inda ta ce ta yanke shawarar rabuwa da kocin ne a yammacin ranar Asabar bayan ta sha kashi da ci 3-1 a Valencia. Wannan ne karo na shida da aka yi rashin nasara a wasanni bakwai na gasar.

Granada ta cigaba da zama ta 17, maki uku sama da Alaves mai matsayi na 18.

Advertisement

Sanarwar ta ce “Kungiyar ta yanke shawarar a wannan Asabar don korar kocin kungiyar ta farko.” “Muna so mu gode wa Robert Moreno saboda aikinsa da sadaukarwarsa a wannan lokacin kuma muna yi masa fatan alheri a nan gaba.”

Kulob din ya kuma fuskanci wulakanci a gasar cin kofin Spaniya lokacin da Atletico Mancha Real mai mataki na hudu ta fitar da ita a watan Disamba.

Ruben Torrecilla, mai horar da ‘yan wasan ajiye, ya karbi ragamar kungiyar ta farko na wucin gadi.

Advertisement