Siyasa

Goodluck Jonathan bai fice daga PDP ba – Omokri

Shahararren mai fafutukar siyasa da zamantakewa a Najeriya, Reno Omokri, a ranar Lahadi, ya mayar da martani kan rahotannin da ke cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fice daga jam’iyyar PDP.

Omokri ya bayyana rahotannin cewa Jonathan ya fice daga PDP a matsayin karya.

A cikin jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon mai taimaka wa Jonathan ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da rahoton.

Advertisement

A cewar Omokri: “Labarin da ke yawo a kai cewa tsohon shugaban kasa @GEJonathan ya yi murabus daga @OfficialPDPNig karya ne. Ƙarya ce sosai!

“Mutanen da aka ƙi a jiharsu ne ke yawo da wannan labarin kuma suka je garin ubangidansu don karɓar karramawa. Yi watsi da shi.”

Ya kuma bayyana tsohon shugaban a matsayin mutum mai tsayayye wanda ya kasance dan jam’iyya daya a tsawon rayuwarsa.

Omokri ya jaddada cewa Jonathan baya tsalle daga wannan jam’iyya zuwa waccan.

“Sule Lamido, ba abin da za ka ji tsoro. Tsohon shugaban kasa Jonathan yana da shekaru 64 a duniya. A tsawon rayuwarsa, dan jam’iyya daya ne kawai.

“Halinsa daban ne. Yana da kwanciyar hankali. Ba ya tsalle daga jam’iyya zuwa jam’iyya. Ka huta, Malam Lamido,” ya kara da cewa.

Advertisement