Addini

Gaskiyar magana game da jita-jitar cewa an kama Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto

A wannan Assabar ne ƴan Najeriya suka tashi da wasu labarai da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa jami’an tsaron kasar sun kama Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto bisa dalilin goyon bayan sa ga kisan da aka yiwa Deborah Samuel.

Deborah dalibar kwalejin ilimi ta Shehu Shagari ce da ake Sakkwato wacce ta yi batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

A wata sanarwa da ya fitar Shugaban Media na malam, Malam Mustapha Bashir Albaniy ya musanta wadannan labarun, acikin sanarwar ya bayyana cewa malam yana gidan sa tare da iyalinsa lafiya ba abinda ya same shi.

Advertisement

“Ko ɗan yatsa babu wanda ya nuna masa kawo yanzu:” Inji Shi.

Allah ya tsare muna imanin mu.

Advertisement