Maganin Ƙurajen Fuska Da Abubuwan Da Ke Janyo Su

Kurajen fuska ko (Pimples) a turance wasu kuraje ne da suka fi fitowa a fuskar mutum musamman idan mutum yana ta’ammali da mayukan shafawa iri-iri ba tare da kula da wanda daya dace da fatar shi ba.

Matsalar kurajen fuska tafi shafar mata musamman matasa inda za’a ga wasu matan har nikab suke sanyawa a fuskokin su saboda kar aga ta’adin da kurajen na ‘Pimples’ suka yi musu a fuska.

Maza ma sukan fuskanci irin wannan matsala ta ‘Pimples a fuska sosai a wani lokaci na rayuwar su.

Kadan daga cikin Abubuwan dake janyo kurajen fuska sun hada da;

• Yawan cin Abu mai maiko.
• Amfani da mayukan da Basu dace da fatar fuska ba.
• Kwayoyin cuta.
• Shiga rana sosai.

Mutane da dama kan kashe makudan kudade don sayan maganin da zai magance musu kurajen na fuska amma kuma yawanci ba’a samun waraka.

Saboda haka muka ga ya dace mu bayyawa yan uwa da wasu hanyoyi da insha’Allah idan aka bi su za’a samu sauƙin wannan matsalar sosai.

Yadda za’a yi maganin wannan matsalar sune maka bayyana a kasa, kuma a tabbatar an waɗannan hanyoyi daidai gwargwadon iko domin cimma biyan bukata. Abubuwan sune;

Bawon lemon zaki: Ana shafa bawon lemon zaki a inda kurajen suka fito sai a bar shi ya kwana da safe sai a wanke da ruwa masu dan zafi-zafi.

Zuma: Za’a samun zuma mai kyau a goga da auduga akan kurajen na ‘Pimples’, sannan a bar zuwa yan mintuna kamar 30 sai a wanke. Za’a iya maimaitawa kamar sau biyu a rana har kurajen su mutu.

Ruwan lemon tsami: Ruwan lemon tsami wata sahihiyar hanya ce mai matukar amfani wajen maganin kurajen fuska ‘Pimples’.

Lemon tsami yana taka rawar gani sosai wajen kashe kananan kwayoyin cuta a fuska da kuma fitar da maikon fuska. Yadda za’ayi amfani da lemon tsami shi ne a samu lemon tsami a matse ruwansa sai a samu auduga mai tsafta a dinga goge fuska dashi kafin a kwanta bacci, da safe sai a wanke fuskar da ruwan dumin. Za’a iya maimaitawa sau biyu ko uku a rana har kurajen su fita.

Ganyen darbejiya / Man darbejiya:
Ana kwaba ganyen darbejiya da man darbejiya a shafa a fuska zuwa mintuna biyar sai a wanke da ruwan dumi ko a dinga shafa man darbejiya da auduga a fuskar har zuwa lokacin da kurajen zasu baje.

Kurajen fuska dai sun dade suna batawa mutane fuskokin su har ta kai wasu ma sun gaji da nemawa kansu magani, mata ma kan yi duk yadda zasu yi su rufe fuskokin su don kar a ga kurajen, wasu ma kanyi amfani da hodar foundation akai akai don boye kurajen dake fuskar su.

Wadannan hanyoyi muka lissafa da karin wasu zasu taimaka sosai wajen cire kurajen fuska cikin sauki ba sai mutum ya kashe makudan kudade ba wajen neman magani asibiti ba.