Tsaro

Ganduje ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wata mata da aka kashe a Kano

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci jami’an tsaro da su gaggauta bankado wadanda suka kashe Rukayya Mustapha, matar aure da wasu yan bindiga suka kashe.

Gwamnan yayi wannan kiran ne a ranar Litinin a lokacin da yake jajantawa iyalan mamaciyar a unguwar Dorayi Quarters dake karamar hukumar Kumbotso a jihar.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakin shi Dakta Nasiru Yusuf Gawuna yace gwamnatin Kano ta dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano.

Advertisement

“A cikin tsananin kaduwa muka samu labarin rasuwar Marigayi Rukayya Mustapha… Ina mai tabbatar muku da cewa ba za mu bar wani abu ba wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar”.

“A madadin gwamnati da al’ummar jihar ina Allah wadai da wannan aika-aika tare da addu’ar Allah ya jikan ta da Jannatul Firdaus tare da baiwa ‘yan uwanta kwarin guiwar jure rashin Ganduje ya ce”.

A nasa bangaren, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bayyana cewa kawo yanzu an kama mutane 5 da ake zargi, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo wadanda suka kashe.

Ya kuma yi nuni da cewa, wadanda suka yi ta’ammali da miyagun kwayoyi ne suke aikata irin wadannan laifuffuka, shi ya sa suke kame wadanda suka yi safarar miyagun kwayoyi domin dakile sake afkuwar lamarin.

Dikko ya kuma bayar da tabbacin cewa, hukumomin tsaro za su rubanya kokarinsu na ganin an tabbatar da faruwar irin wadannan laifuka.

Tawagar ta kunshi kwamishinoni, Daraktan DSS Alhassan Muhammed da shugaban karamar hukumar Kumbotso Hassan Garban Kauye.

Advertisement